A cikin wata sanarwa da ya fitar, jagoran matasan na jam'iyyar ADC, Hon. S.A. Saminu Shehi Kura ya bayyana matuƙar farin cikin sa bisa s...
A cikin wata sanarwa da ya fitar, jagoran matasan na jam'iyyar ADC, Hon. S.A. Saminu Shehi Kura ya bayyana matuƙar farin cikin sa bisa shiga jam'iyyar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi, inda ya ce shigowar Kwankwaso da cewa ba ƙaramin abu ba ne ga jam’iyyar ADC, musamman duba da irin ƙwarewa, gogewa da kuma tasirin da yake da su a fagen siyasa.
Hon. Shehi ya ƙara da cewa, wannan mataki na Kwankwaso zai ƙara ƙarfafa gwiwar matasa da sauran al’umma wajen rungumar sabuwar tafiya ta siyasa da jam’iyyar ADC ke gabatarwa, wacce ta ke mayar da hankali kan gaskiya, adalci da kuma ci gaban ƙasa.
Hakazalika, Shehi Kura ya bayyana cewa shigowar Sanata Kwankwaso abin alfahari ne ga al’ummar Nijeriya, domin zai taimaka wajen samar da ingantaccen shugabanci da kuma kawo sauyi mai ma’ana a harkokin mulki.
A ƙarshe, ya yi kira ga matasa da sauran ‘yan ƙasa da su mara wa jam’iyyar ADC baya, domin ciyar da ƙasa gaba da kuma gina kyakkyawar makoma ga al’umma baki ɗaya.

No comments