Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya ɗaukacin mabiya addinin Kirista murnar bikin Ista wanda aka fara a yau...
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a wannan rana ta Juma’a, Idris ya ce:
“Ina taya dukkan ’yan’uwan mu Kiristoci murnar rungumar saƙon Ista na kyakkyawar fata, sabuntawa, da sadaukarwa.
“Wannan lokaci yana tunatar da mu ƙarfin ban-gaskiya wajen shawo kan duk wani ƙalubale, tare fatan ganin sababbin al'amurra na alheri.
“Allah ya sa wannan lokaci ya ƙarfafa dangantakar haɗin kai da ta haɗa mu a matsayin ƙasa ɗaya al'umma ɗaya, kuma ya zaburar da mu mu ci gaba da gina Nijeriya inda zaman lafiya, haƙuri da juna, da kyakkyawar niyya za su bunƙasa.
“Barka da Ista ga dukkan masu bikin, a gida da waje.”

No comments