Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Ci Gaba Da Bayar Da Gudumawa Don Tabbatar Da Nasarar ADC A Kano -Ambasada Mainasa

Daga Ibrahim  Muhammad, Kano A yayin da jam'iyyar ADC ke ci gaba da samun karbuwa da samun shigowar muhimman mutane manyan jagororin siy...

Daga Ibrahim  Muhammad, Kano

A yayin da jam'iyyar ADC ke ci gaba da samun karbuwa da samun shigowar muhimman mutane manyan jagororin siyasa cikin ta daga jam'iyyu daban-daban, wani jigo a cikin jam'iyyar da ya daɗe yana bada gudumawa wajen bunʙasata a jihar Kano daga ʘaramar Hukumar Dala, Ambasada Abdulrahman Mai Nasara Salga ya bayyana jin daɗin sa da yadda jam'iyyar ke samun karbuwa.

Ambasada Abdulrahman Salga, wanda ya yi takarar neman ɗan majalisar tarayya a ʘaramar Hukumar Dala a 2023, ya ce abin farin ciki ne garesu irin bunʙasar da ake samu a jam'iyyar da suka jima suna ʙoʙarin ganin ta karbu ta tallata manufofin ta a tsakanin jama'a.

Ya ce, shigowar Dakta Rabiu Musa jagoran Kwankwasiyya da ɗumbin magoya bayan sa, tare da shigowar tsohon mataimakin Gwamnan Kano, ʘwamared Aminu Abdulsalam, da dan takarar Gwamnan Kano a jam'iyyar APC a zaben 2023, Dokta Nasir Yusuf Gawuna, jam'iyyar ADC a nan Kano babban ci gaba ne da nasara ga jam'iyyar da ake ganinta ʙarama ce a baya, yanzu ta zama jam'iyyar adawa mafi ʙarfi a ʙasar nan.

Abdulrahman Mainasara ya ce su a matsayin su na yan jam'iyyar za su ci gaba da abin da suke yi na ganin al'umma sun karbe ta, suna fata jiga-jigan shugabanni da suke a jam'iyyar tun daga kan tsohon mataimakin shugaban ʙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Kwankwaso da sauran jagorori za su haɗa kai, a sanya mafitar ʙasar nan a gaba domin kai wa ga nasara a zaben 2027 mai zuwa.
 

No comments