Daga Zubairu Lawan, Lafia Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP a zaɓukan shekarun 2019 da 2023, Mista David Ombugadu...
Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP a zaɓukan shekarun 2019 da 2023, Mista David Ombugadu, ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar APC mai mulki ne domin taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, amma an hana magoya bayan sa yin rajista, wanda hakan ta tilasta masa ficewa.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da 'yan Jarida a garin Lafia ranar Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026.
Hon.Ombugadu, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa zuwa APC, amma bayan wasu makonni kaɗan ya sake ficewa ya koma PDP bisa zargin nuna wariya, ya ce a shirye yake ya taimaka wa Shugaba Tinubu a 2027, amma an hana magoya bayan sa yin rajista a tsarin e-registration na APC.
Ya bayyana cewa ya roƙi jam’iyyar da ta buɗe wata hanya (portal) domin yin rajistar mambobin sa da suka fice daga jam’iyyar adawa suka shiga APC, amma aka ƙi ba shi wannan dama.
“Ban nemi a ba ni wani muƙami a jam’iyyar ba, ko shugaban mazaba ko sakatare ban nema ba. Abin da na nema kawai shi ne a yi wa mambobina rajista, amma aka ƙi, shi ne dalilin da ya sa na sake barin APC,” in ji shi.
Sakamakon haka, Ombugadu ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Ya ce ya dawo PDP da cikakken ƙarfi, inda ya ƙara da cewa, “Muna da jama’a, kuma muna da tsari (blueprint) da zai inganta rayuwar al’ummar jihar da ma ƙasar baki ɗaya idan aka zaɓe ni gwamna a 2027.”
Ombugadu ya kuma yi bayani dalla-dalla kan nasarorin da ya samu a fannoni kamar samar da ruwa, aikin yi, tallafawa jama’a, lafiya da sauransu lokacin da yake mamba a Majalisar Wakilai, inda ya ce zai bunƙasa jihar idan aka ba shi dama a 2027.
Haka kuma ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa a zaɓen cike gurbi (bye-election) domin samun damar kawo ayyukan ci gaba a yankin.
Ya jaddada cewa burinsa na Sanata ba na 2027 ba ne, sai dai na 2026.
“Zan tsaya takarar zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa. Zan shiga Majalisar Dattawa a 2026, sannan kuma in sake tsayawa takarar gwamna a 2027,” in ji shi.
Don haka, ya roƙi goyon bayan al’ummar Nasarawa ta Arewa da ma jihar baki ɗaya domin samun nasara.
A nasa jawabin, Mista Francis Orogu, Mataimakin Shugaban PDP na ƙasa mai kula da yankin Arewa ta Tsakiya, ya buƙaci al’ummar jihar da su mara wa jam’iyyar baya domin samun nasara.
Haka kuma ya nuna cikakken goyon baya ga Ombugadu domin ya cimma burinsa.

No comments