A ci gaba da ƙoƙarin ta na magance safarar mutane, musamman yara ƙanana, Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta ƙasa (NAPTIP) reshen jihar...
Waɗannan ma'aurata da kotun ta samu da laifi, Madam Esther Ini Udo da mijinta Eyo Stephen Udo, sun fuskanci tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi saye da sayar da jarirai, wanda hakan ta saba da dokar hana fataucin mutane ta shekarar 2015.
A wasu bayanan da aka gabatar a gaban kotun tarayya da ke Calabar, matar ta sayar da jaririn ta da ta haifa kan kuɗi Naira dubu 300 ga wata mai suna Oluchi Judith, wanda ya tsere, kuma hukuma ke nema ruwa a jallo.
Haka kuma, an bayyana cewa ma’auratan sun sayi wani yaro mai shekara guda kan Naira dubu 150 daga wasu mutane biyu, sannan suka sake sayar da shi kan Naira dubu 400 ga wannan mata.
Kotun ta nuna matuƙar damuwa kan wannan aiki, tana mai jaddada cewa safarar jarirai babban laifi ne da ke tauye haƙƙin bil’adama.
Duk da cewa waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin a farko, kotun ta same su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen da aka gabatar musu.
Mai shari’a I. Ojukwu ya yanke wa kowannen su hukuncin ɗaurin shekaru 15 tare da tarar Naira miliyan biyu, inda aka ce hukuncin zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2026.
Haka zalika, kotun ta umurci hukumar NAPTIP da ta kamo Oluchi Judith domin gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin hannu a wasu laifukan fataucin mutane.

No comments