Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami...
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami'o'in ƙasar.
Ministan ilimin ƙasar, Tunji Alausa ne ya bayyana haka ranar Talata a lokacin taron tsara fitar da guraben karatu na 2025 a ƙasar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Za a shigar da ƙa'idar cika shekara 16 a cikin manhajar hukumar JAMB da ke tantance ƙa'idojin bayar da gurbin karatu.
Haka kuma Ministan ya ce za a yi la'akari da ɗaliban da za su cika shekara 16 ranar 31 ga watan Agustan 2025.
A Najeriya ana samun yawan ƙorafi kan bai wa ƙananan yara guraben karatu a jami'o'in ƙasar, wani abu da masana ke cewa zai shafi fahimtarsu da kuma yadda za su iya jure wa wahalhalun karatun jami'a.
No comments