Wani malami da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, malamin Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Auchi, an same shi tsirara a ɗakin wata matar au...
Wani malami da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, malamin Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Auchi, an same shi tsirara a ɗakin wata matar aure.
Dubunsa ya cika ne a lokacin da yake tsaka da lalata da matar auren a cikin gidan aurenta, inda jama'a suka antayo cikin ɗakin kai tsaye.
A cikin wani faifan bidiyo da yanzu haka yake zagayawa a shafukan sada zumunta, an ga malamin a tsirara, kewaye da fusatattun mutane, ciki har da mijin matar, ana dukan sa ana cewa ya buɗe fuskarsu.
An ji shi yana kuka na nadama yayin da waɗanda suka fallasa lalatarsa suke wulaƙanta shi.
Wani mutum da ke ba da labari a bayan fage ya yi ikirarin cewa lamarin ya faru ne a cikin ɗakin kwanan matar, kuma malamin ya ziyarci gidan ne musamman domin ya yi lalata da ita ya ba ta maki a matsayinta da ɗalibarsa a Polytechnic ɗin.
An ce matar ta haihu kwanan nan ne ƙasa da watanni biyu da suka wuce, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura game da lokaci da kuma wurin da ake zargin an aikata laifin.
Har yanzu dai ba a san ko an kama malamin kafin ko kuma bayan ya gama lalatar, amma wurin da aka xauka a cikin bidiyon ya sa yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta suka firgita tare da nuna ƙyama.
Har yanzu ba a bayyana sunan matar da mijinta ba.
Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Auchi, har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto.
No comments