A cikin sa’o’i 24 bayan harin da aka kai fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ke gidan Rumfa, Ƙofar Kudu, a cikin birnin Kano, wasu ƙun...
A cikin sa’o’i 24 bayan harin da aka kai fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ke gidan Rumfa, Ƙofar Kudu, a cikin birnin Kano, wasu ƙungiyoyin farar hula da ke ƙarƙashin jagorancin One KANO Agenda, sun buƙaci a hukumomin tsaro, musamman ‘yan sanda, da su fitar da bayani kan shiru da suka yi game da lamarin.
An rawaito cewa wata tawagar tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ce ta kai harin a daren Lahadi, a yayin da take dawowa daga gidan marigayi attajirin Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, bayan kai gaisuwar ta’aziyya.
Bayanan da ƙungiyoyin suka tattara dai sun yi nuni da cewar tsohon sarkin ya bar hanyarsa ta yau da kullum da ke kai shi Mandawari, ya karkata ta Kabara wadda ke gaban fadar Gidan Rumfa, wanda hakan ya janyo harin da wasu da ake zargin na cikin 'yan rakiyarsa ne suka kai.
Ƙungiyoyin farar hular da suka haɗa kai ƙarƙashin jagorancin One KANO Agenda, sun bayyana shiru da jam’ian tsaro suka yi a matsayin abu mai tayar da hankali wanda ke nuna gazawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar, kuma yana iya haifar da ruɗani da fitina.
Sun ce hakan na iya zama wani yunƙuri na daban don Kawo Rashin Zaman Lafiya da gangan a Jihar Kano.
Ƙungiyoyin sun kuma bayyana Rahoton Abubuwan Da Aka Lalata da Wanda Aka Sata Kamar Haka :
Motocin 'Yan Sanda:
Hilux ta 'yan sanda (NPF 182D) – Mopol 9.
Hilux ta 'yan sanda (NPF 195D) – Mopol 52.
Abubuwan da aka lalata:
Babur na Abdullahi Shehu (Jami’in ‘yan sanda)
Babur na Ibrahim Isa (Mashal din tsaro a masarautar)
Babbar ƙofa ta ƙarfe ta masarautar ta lalace matuƙa.
Wurin tsaron 'yan sanda da ke fadar Shima an lalata shi.
Kayan Tsaro da Aka Sata:
Cikakken kayan 'yan sanda na kamfale.
Takalman tsaro na 'yan sanda guda ɗaya.
Majigin harsashi ɗaya – wanda ke da matuƙar hatsari.
Mutanen da suka jikkata:
Maigoma Dan'agundi (yana kwance a Asibitin Murtala Muhammad).
Yunusa Babba (Mashal ɗin tsaro).
Murtala Muhammad (Jami’in ‘yan sanda na musamman).
Abin da muke buƙata:
1. A gaggauta fara bincike kan harin da aka kai, Sannan a yi nazari akan abin da aka lalata kamar dukiyoyin gwamnati da kuma kai hari ga jami’an tsaro da fararen hula.
2. A gano, a kama, sannan a gurfanar da duk masu hannu akan kai wannan hari.
3. A nemo kayan ‘yan sanda da aka sata, musamman majigin harsashi wanda ke da babbar barazana ga tsaro.
4. A ƙara tsaurara tsaro a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ma gidansa baki ɗaya.
Muna kira ga hukumomin tsaro a Kano da su ɗauki matakin gaggawa da na kwarjini don kare doka da oda, da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Doka ba za ta amince da aikata laifi ba, kuma babu wanda ya fi doka, ko da kuwa yana da matsayin mulki ko iko.
Waɗanda suka rattaba hannu:
Mustapha Abdullahi – Kano Digital Media Rangers.
Comrd Salisu Gambo – Youth Mobilization By Media.
Alhaji Suleiman Idris – Northern Youth Assembly.
Malam Abdulƙadir Abubakar – One Voice Development Initiative.
Aisha Muhd Shettima – Beyond Border Alliance.
Barr. Badamasi Gandu – Kano First Forum.
Amb. Abbas Abdullahi – Shugaban ONE KANO AGENDA.
Barr. Mukhtar Musa – Sakataren ONE KANO AGENDA.
No comments