Rikicin da ya barke a Masarautar Kano ya haifar ya zo da sabon salo a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da magoya bayan Sarkin Kano na 15, A...
Rikicin da ya barke a Masarautar Kano ya haifar ya zo da sabon salo a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da magoya bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, suka ƙaddamar da wata zanga-zanga a fadar Kofar-Kudu na Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II.
Wani rahoto da jaridar The Guardian ta wallafa ya ce, wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da sarki Bayero da muƙarrabansa ke dawowa daga gidansa na Mandawori.
Wata sanarwa da ƙungiyar yaɗa labarai ta Masarautar Kano ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sadam Yakasai kuma ta mika wa jaridar The Guardian, ta bayyana cewa an kai harin ne a lokacin da Sarki Sanusi ke wajen fadar.
Yakasai ya ce, “Sun fasa Æ™ofar ne suka far wa masu gadin, inda suka jikkata wasu daga cikinsu, suka farfasa motocin ‘yan sandan da ke cikin fadar, da gangan Aminu ya bi ta titin fadar sarki maimakon ya bi hanyar da ta dace daga Koki zuwa Nassarawa, wanda hakan ya sa ‘yan daba suka yanke shawarar kai hari Gidan Rumfa.
“Wannan ba shi ne karon farko da ya ratsa yankin ba, ya yi hakan ne a baya-bayan da ya ziyarci gidan sa na Mandawari, ya yi hakan ne domin ya tsoratar da mutanen yankin,” inji Yakasai.
Yakasai ya dage kan cewa sarki na 15 bayan gwamnatin jihar Kano ta tsige shi, ya koma da zama tare da kwace karamar fadar Nassarawa, inda ya ketare iyaka ba tare da taka tsantsan ba.
“Bai yi kalubalantar tsige shi a wata kotu ba, amma yana dogara ne da wasu da suka yi hakan, gwamnan ya nuna kamun kai da kishin kasa duk da tashin hankalin da hambararren sarkin da ‘yan barandan sa suka yi a unguwar gidan gwamnati.
“Kazalika a lura cewa korarren Sarkin ba shi da goyon bayan ko daya daga cikin masu ruwa da tsaki a masarautun, domin hakimai 37 daga cikin 38 sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi.
“Daya ne kawai daga cikin ’yan’uwan Aminu Ado Bayero shida da ba su yi mubaya’a ba, ko da dan uwan tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ne a kwanakin baya Sarki Muhammad Sanusi II ya nada shi Hakimin Ganduje, maimakon Aminu Ado Bayero da ke ikirarin shi ne sarki.
“Wannan shi ne karon farko da hambararren Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ke kai yakinsa kai tsaye Gidan Rumfa yayin da yake ci gaba da zama a gidansa da ke da tsaro a fadar Nassarawa, kusa da fadar gwamnatin jihar Kano,” in ji Yakasai.
Sai dai kokarin jin ta bakinsa a fadar Nassarawa ya ci tura, domin mai magana da yawun Sarkin na 15, Abubakar Kofar-Naisa, bai amsa kiran da aka yi masa a wayarsa ba.
Sai dai wani shaida a kan lamarin, Muktar Dahiru, ya karyata labarin Yakasai, ya kuma dage cewa lamarin ya kasance rikici ne tsakanin wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan bata-gari a fadar Kofar-Kudu da kuma magoya bayan Bayero.
Dahiru, wanda ke cikin tawagar Bayero, ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da wasu ‘yan bata-gari da ba a san ko su wanene ba suka yi amfani da muggan makamai suka kafa shingen hana sarki na 15 wucewa ta Kofar-Kudu, ya bada misali da tawagarsa.
Shaidan, wanda ya dage cewa bai da masaniyar wani mai gadin fadar da ya samu rauni, sai dai ya tabbatar da dakile yunkurin wasu barayin da ba a san ko su waye ba na tare hanyar Bayero.
Ya jaddada cewa rikicin ne ya sa ‘yan sanda suka shiga tsakani, inda suka tarwatsa ’yan bindigar da hayaki mai sa hawaye.
“Ina tare da tawagar Sarkin Kano Alh. Aminu Bayero a lokacin da lamarin ya faru, a gaskiya muna tahowa daga unguwar Koki inda muka kai ziyarar ta’aziyya gidan iyalan Alhaji Aminu Dantata.
“Amma a lokacin da muka dawo fadar Nassarawa ta Kofar-Kudu, sai muka ga wasu ‘yan iska sun tare hanya a kofar fadar, suna dauke da muggan makamai, a lokacin sai magoya bayan sarki Bayero suka tunkare su don share hanyar, kuma sun yi nasarar hakan, kuma Sarkin Bayero ya yi tafiyarsa ba tare da wani rauni ba.” Inji Dahiru.
No comments