Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Datti Baba-Ahmed Martani Kan Sukar Da Ya Yi

 Ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya mayar da martani ga kalaman Sanata Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iy...


 Ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya mayar da martani ga kalaman Sanata Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a 2023, wanda ya yi suka kan matakin da shugaba Tinubu ya ɗauka na ci gaba da barin mataimakin sa Kashim Shettima akan karagar sa.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun Mataimakin Shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha, ofishin ya bayyana kalaman na Baba-Ahmed a matsayin "kalamai marasa kan gado" waɗanda shugaban ƙasa da mataimakin sa ba su da lokacin sauraron su, kasancewar sun mayar da hankali kan ayyukan su na gina ƙasa.

Sanarwar ta kuma bayyana irin nasarorin da mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya samu da ma ƙwarewar sa akan aiki da ta haɗa da gogewar sa a harkar koyarwa da bayar da ilimi da kasancewar sa ma’aikacin banki, sannan kwamishina, sannan gwamna, kana sanata, kafin ya zama Mataimakin Shugaba ƙasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Shettima na biyayya ga shugaba Tinubu kamar yadda yake nuna jajircewar sa kan tabbatar da ajandar sabunta fata ta Renewed Hope a turance.

Ofishin ya kuma tunatar da Baba-Ahmed abubuwan da suka faru a baya, da suka haɗa da cire shi daga majalisar dattawa a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da maguɗin zabe inda ta ƙara da cewa, zantukan na Baba Ahmed watakila ba za su rasa nasaba da kwaɗayin sa na ɗarewa kowace irin kujerar mulki ba ko da kuwa ta haramtacciyar hanya ce, musamman ma kujerar Mataimakin Shugaban ƙasar wadda Datti Baba-Ahmed ɗin ya sha kaye a takarar ta a zaɓen bara sakamakon karawar sa da gogaggen ɗan siyasa ɗan asalin Arewa wanda ke da tarin abin faɗa na nasarori a ajandar sabunta fata ta Shugaban Kasa.

No comments