Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa Za Su Dara, Tinubu Zai Samar Masu Da Ayyukan Yi Miliyan 5 A Fannin Kiwo Kaɗai– Jega

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara, kuma shugaban kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi, Farfesa Attahiru Jega, ya yi garg...


Mai bai wa shugaban ƙasa shawara, kuma shugaban kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargaɗin cewa Nijeriya na iya fuskantar kasadar ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara, idan har ba a aiwatar da tsarin sake fasalin kiwon dabbobi na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Ya kuma bayyana cewa, a ƙoƙarin da ake yi na cike gibin da ake da shi a bangaren abinci mai gina jiki, Nijeriya na kashe maƙudan kuɗaɗe da suka tasamma Naira biliyan 1.5 a duk shekara, wajen shigo da kayan kiwo; wanda galibi madara ta fi yawa, wadda ke da kuma ƙarancin sinadarin gina jiki.

Haka zalika, Jega ya ce; “Daga nan zuwa shekarar 2030, idan ya kasance an aiwatar da tsare-tsare da kuma gyare-gyare a kan kiwon dabbobi na shirin Shugaba Tinubu, Nijeriya za ta samu nasarar ƙirƙiro ayyukan yi kusan kimanin miliyan biyar ga matasa, ta fuskar samar da wadataccen nama, kiwo, fata da sauran kayan da kamfanoni ke buƙata, musamman don taimaka wa matasa da mata a yankunan karkara da birane, wajen samun ayyukan yi.”

Wannan dai na zuwa ne, daidai lokacin da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Saliu Mustapha, ya ba da shawarar ware kashi 6 cikin 7 na kasafin kudin Nijeriya, domin samar da ayyukan yi a kasar.

An gudanar da laccar wannan shekara ta 2025 ne kamar yadda aka saba yi a kowace shekara, ranar Litinin da ta gabata a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, don girmama wani dan majalisa.
 

No comments