Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YAƘI DA TA'ADDANCI: Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa Dakarun Mu - Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da walwala da samar da kayan yaƙi ga rundunar sojin Nijeriya don...

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da walwala da samar da kayan yaƙi ga rundunar sojin Nijeriya don ci gaba da yaƙar ta'addanci

Da yake jawabi a wajen bikin zagayowar ranar sojoji karo na 162 a Kaduna, Tinubu wanda mataimakin sa, Kashim Shettima ya wakilta, ya tabbatar wa sojojin da cikakken goyon bayan sa wajen tunkarar ‘yan ta’adda da kuma fatattakar su.

Shugaban ya misalta  ƴan ta'addan da marasa imani, da ba su martaba addini ko ƙabila, inda ya ce gwamnatin sa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙar su

Shugaban ya yi alƙawarin ci gaba da saka hannun jari a fannin samar da kayan aikin soji na zamani, da kafofin bayanan sirri, da samar da walawala ga rundunar don tabbatar da cewa jami’an ta ba su rasa makamai da ƙwarewa ba.

Shugaban ya amince da ƙalubalen tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummar ƙasar, waɗanda suka haɗa da ta’addanci, tayar da ƙayar baya, da ‘yan fashin daji  da masu tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya kuma buƙaci sojojin Nijeriya da su ƙara zage damtse tare da ba su tabbacin  cikakken goyon bayan sa da na ‘yan Nijeriya.

Shugaban ya jinjina wa jaruman da suka riga mu gidan gaskiya tare da jajanta wa iyalansu, inda ya ba su tabbacin ci gaba da tunawa da su na har abada.

“Kuna da cikakken izinina da na al’ummar Nijeriya kan fatattakar masu zagon ƙasa a ƙasar mu.”

"Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, kada mu miƙa makomarta ga rarrabuwar kawuna, ko nuna halin ko-in-kula," in ji Tinubu.

Taron ya samu halartar manya da dama da suka haɗa da tsohon shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon, gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, da Ministocin Tsaron Nijeriya, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, sai shugaban Hafsan soji Laftanar Janar Olufemi Oluyede.
 

No comments