Jami’ar Jihar Borno da ke Maiduguri, tare da wasu manyan makarantu daga Arewacin ƙasar nan, sun tabbatar da karɓar tallafin kuɗi daga Asusun...
Jami’ar Jihar Borno da ke Maiduguri, tare da wasu manyan makarantu daga Arewacin ƙasar nan, sun tabbatar da karɓar tallafin kuɗi daga Asusun Lamunin Karatu na Ƙasa (NELFUND) domin sauƙaƙa wa ɗalibai biyan kuɗin makaranta a zangon karatu na 2024/2025.
Shugaban jami’ar Borno, Farfesa Babagana Gutti, ne ya bayyana cewa jami’ar ta tantance dalibai 3,644, kuma ta karɓi kuɗi har naira miliyan 253,760,300 daga gwamnatin tarayya, domin biyan kuɗin makaranta na waɗannan ɗaliban a ƙarƙashin shirin NELFUND.
Haka kuma, Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a Jihar Jigawa, ta samu tallafin kuɗi har ₦110,312,250 domin ɗalibai 3,512, kamar yadda Dr. Abba Auwalu, shugaban kula da harkokin ɗalibai na jami’ar, ya tabbatar.
A nata ɓangaren, Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Potiskum, ta karɓi ₦73,429,200 don ɗalibai 1,130 da aka tantance kuma suka cancanci samun wannan tallafin.
Wannan mataki dai ya biyo bayan ƙudurorin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na tabbatar da cewa ba ɗalibi ɗaya ba zai bar karatu saboda rashin kuɗin makaranta, musamman daga cikin iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Shirin na NELFUND na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na farfaɗo da harkar ilimi tare da samar da damar ilimi ga kowa da kowa ba tare da la’akari da matakin rayuwa ba.
No comments