Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MARIGAYI ƊANTATA: Kashin Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Zuwa Kano Don Isar Da Ta'aziyya

A ci gaba da nuna alhinin ta kan rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata, gwamnatin tarayya ta tura wata ƙaƙƙarfar tawaga a ƙarƙashin jagoranc...


A ci gaba da nuna alhinin ta kan rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata, gwamnatin tarayya ta tura wata ƙaƙƙarfar tawaga a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima don isar da ƙarin ta'aziyya a ci gaba da zaman makokin Marigayin da ke gudana a gidan sa da ke birnin Kano.

Tawagar, wacce ta ƙunshi manyan Jami'an gwamnati, kamar mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia; Mai bai wa shugaban kasa shawara kan ayyuka na kasa, Dr. Aliyu Modibbo; da kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Dr. Mohammed Bello Adoke sun sami tarba daga gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, tare da manyan jami'an gwamnatin jahar  inda suka dunguma zuwa gidan Marigayin.

Mataimakin shugaban kasar ya gabatar da addu’ar Allah Ya jaddada Rahma ga Marigayin  tare da tabbatar wa da iyalan marigayin cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da su a wannan lokaci na jumami da ma bayansa
 

No comments