Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ma'aikatan Bankin KEYSTONE Sun Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga iyalan Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugabanni da ma'aikatan bankin kasuwanci na Keystone sun bayyana cewa rashin Alhaji Aminu Ɗantata babban ra...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugabanni da ma'aikatan bankin kasuwanci na Keystone sun bayyana cewa rashin Alhaji Aminu Ɗantata babban rashi ne, ba kawai ga al'ummar jihar Kano ba, rashi ne na Nijeriya, Afirka da ma Duniya ma baki ɗaya, musamman bisa la'akari da irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban rayuwar al'umma a bangarori da dama.

Shugaban Cibiyar Ma'aikatan Banki na Nijeriya reshen jihar Kano, wato 'Chartered Institute of Bankers of Nigeria', wanda ya ke kuma shi ne Babban Daraktan Bankin Keystone na yankin Arewa Abubakar Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci ma'aikatan zuwa ziyarar ta'aziyyar.

Ya ca a madadin dukkan ma'aikatan bankin na Keystone suna miƙa ta'aziyya ga iyalan Alhaji Aminu Ɗantata wanda ba ƙaramin rashi aka yi ba, sai dai a yi addu'ar Allah ya gafarta masa.

Ya ce, abubuwan da za a riƙa tuna Alhaji Aminu Ɗantata da su, ba za su ƙirgu ba domin, rayuwa ce da ya yi ta  hidima da taimako ga al'umma da bunƙasa harkar kasuwanci da gina ɗan'adam da taimakon addini.

Babban Daraktan na bankin Keystone ya ce, za a ci gaba da tuna Marigayin Alhaji Aminu Ɗantata da harkar kasuwanci da ya bunƙasa a matakin Kano da matakin Nigeriya da ƙasashen Duniya, da yadda yake tallafa wa mutane.

A ƙaeshe sun yi addu'ar Allah ya albarkaci zuriyar sa su ci gaba da yin abubuwan da ya ɗora su a kai.

No comments