Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya, TCN, ya sanar da samar da wutar lantarki da sabbin taransfoma guda biyu da aka girka a tashar w...
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya, TCN, ya sanar da samar da wutar lantarki da sabbin taransfoma guda biyu da aka girka a tashar wutar lantarki mai ƙarfin kilovolt 330/132/33 da ke Birnin Kebbin jihar Kebbi.
Kamfanin ya fitar da sanarwar ne a ranar Juma'ar 27 ga watan Yuni, 2025.
A yanzu ƙarfin wutar da tashar ke samarwa ya tashi daga 300 MVA zuwa 450 MVA. Hakan na nufin kamfanin zai riƙa bai wa rumbun rarraba wutar lantarki da ke Kaduna ƙarin wutar lantarki har na Mega Wat 120 domin raba wa jihohi irin su Kebbi, Sokoto da kewaye.
Bugu da ƙari kamfanin ya sami damar ci gaba da samar da wutar lantarki a babban birnin Yamai ta Jamhuriyar Nijar wanda a kwanaki kafofin labarai suka ruwaito tana fama da rashin wadatacciyar wutar lantarki.
Wannan nasara ta biyo bayan jajircewar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin cewa Najeriya ta fita daga ƙangin rashin wutar lantarki, wanda an sha jiyo shi ya na nanata yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan samar da ababen more rayuwa a ƙasar wanda wutar lantarki da hanyoyi ke kan gaba a cikin ajandodinsa.
No comments