Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Wani Canjin Da Aka Yi A Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (S...


Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayanai da dabarun yada labarai, ya fitar a jiya Asabar, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda a halin yanzu yake Saint Lucia bai yi wani sabon naɗin muƙami ba.

Sanarwar ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da labarai cewa an sauke Sanata Akume daga muƙaminsa, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne da aka ƙirƙira don cimma wata manufa.

Fadar Shugaban Ƙasar ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin wadannan jita-jita da ba su da tushe da makama.
 

No comments