Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar dattijon ƙasa, jagora a kasuwanci kuma shahararren mai taimakon jama’a, Alh...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar dattijon ƙasa, jagora a kasuwanci kuma shahararren mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, wanda ya rasu da safiyar Asabar yana da shekaru 94 a duniya.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Ɗantata a matsayin babban rashi ga ƙasa, musamman la’akari da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban Ƙasa ya jaddada cewa Alhaji Aminu Ɗantata ya kasance fitaccen ɗan kasuwa mai zurfin basira, wanda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin gwamnati, musamman lokacin da ya rike mukamin Kwamishinan Tsare-tsare da Ci gaba a tsohuwar Jihar Kano.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Alhaji Ɗantata bisa irin ayyukan alherin da ya yi, musamman wajen bayar da tallafi a fannin ilimi da kiwon lafiya. Yana mai cewa ayyukan sa sun shafi rayuwar dubban mutane a fadin ƙasar nan.
Ya kuma bayyana cewa dangantakarsa da marigayin ta kasance cike da shawarwari masu amfani da goyon baya wanda ya karfafa masa gwiwa a lokuta da dama.
Shugaban Ƙasa ya kuma aika da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Ɗantata, Gwamnatin Kano da ɗaukacin al’ummar jihar bisa wannan babban rashi.
No comments