Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kano Da Sarki Sunusi II Sun Halarci jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata A Madina

A Litinin ɗin nan ne da misalin ƙarfe 2 na dare, Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da Mai Martaba Sarki Malam Muhammadu Su...


A Litinin ɗin nan ne da misalin ƙarfe 2 na dare, Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da Mai Martaba Sarki Malam Muhammadu Sunusi II suka tashi zuwa birnin Madinah domin halartar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Tun kafin tafiyar su, wata tawaga ta gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin Ministan tsaro, Alhaji Abubakar Badaru ta isa Madina domin halartar wannan jana'iza, wacce ofishin Jakadancin Nijeriya ya tsara yadda za a gudanar.


Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na farko a tarihin Saudiyya da ƙasar ta ba da izinin kawo gawar wani da ba ɗan ƙasar ba, kuma ba a ƙasar ya rasu ba, domin a binne shi a wannan gari mai albarka na Madina.

Alhaji Aminu Dantata ya rasu ne a ƙasar Dubai, kuma kafin rasuwar sa ya yi wasiyyar a bizne shi a Madina idan hakan ta samu. Bayan rasuwarsa, Gwamnatin Saudiyya ta amince da kawo gawar tasa don a biznewa a Madina, a wani abu da ke da matuƙar daraja.

No comments