Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Abin Da Ya Haɗa Nijeriya Da Gwajin Makamin Nukiliya - Shettima

Mataimakin Shugaba Nijeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za ta ci gaba da aiki da haramcin gwajin makaman nukiliya. Shettima ya bayyana hakan...


Mataimakin Shugaba Nijeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za ta ci gaba da aiki da haramcin gwajin makaman nukiliya.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da tawagar hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ƙarƙashin jagorancin sakataren zartarwarta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Nijeriya kamar sauran ƙasashen Afirka da dama na fama da tarin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziƙi da suka haɗa da fatara da talauci da sauyin yanayi.

Ya ce yanzu babban abin da ke gaban Afirka shi ne ta ga ta shawo kan matsalolin da ke barazana ga wanzuwarta - na fatara da kuma tasirin sauyin yanayi, amma ba batun mallakar makaman nukiliya ba.

A nasa ɓangaren jagoran tawagar hukumar, Dr Robert Floyd, ya yaba da ƙoƙarin Nijeriya wajen cimma muradun hukumarsa.

Sannan kuma ya yaba da shugabancin Nijeriya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen bayar da gudummawar rage gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya, kamar yadda ya ce.

No comments