A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke Ikorodu ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 55 mai suna Abu Aremu a gidan yari bi...
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke Ikorodu ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 55 mai suna Abu Aremu a gidan yari bisa zargin yi wa agolarsa biyu fyaɗe.
Aremu, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume uku da suka shafi lalata da fyaɗe.
Babban Alqalin kotun, B.A. Sonuga, duk da haka, bai ɗauki roƙon wanda ake tuhuma ba.
Ya ba da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali sannan ya ba da umarnin a aika da fayil ɗin zuwa ofishin daraktan ƙararrakin jama’a na jihar Legas (DPP) domin samun shawarar shari’a.
Bayan haka, Sonuga, ya ɗage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 25 ga Satumba, har zuwa lokacin da za a ba da shawarar lauya.
Tun da farko lauya mai shigar da ƙara Isaac Aminu ya shaidawa kotun cewa wanda ake aara ya aikata laifin ne a wani lokaci a shekarar 2022 da misalin ƙarfe 1 na rana a filin Damolapa da ke unguwar Lucky Fiber a Ikorodu.
Aminu ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya yi wa ‘ya’yan matarsa, ‘yar shekara 9 da 'yar shekara 11 fyaɗe a shekarar 2022 yayin da mahaifiyarsu ke tare da shi kuma ya ci gaba da yin musu fyaɗe har mahaifiyarsu ta rasu.
Mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa, wanda ake tuhumar kuma a ranar 20 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 10 na safe a daidai wurin da ake zargin ya yi wa babbar ɗiyar fyaɗe, mai shekaru 24 a yanzu.
Ya ce, laifukan sun ci karo da tanadin sashe na 137 da na 260 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
No comments