Ministan Lantarki a Nijeriya, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin Nijeriya na nazarin ƙarin kuɗin lantarki a kokarin cike giɓin bashin naira ti...
Ministan Lantarki a Nijeriya, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin Nijeriya na nazarin ƙarin kuɗin lantarki a kokarin cike giɓin bashin naira tiriliyan huɗu da ake bin masana'antar.
Adebayo da ke waɗannan bayanai a taron masu ruwa da tsaki a Abuja, ya ce ta wannan hanya kaɗai za a iya ceto masana'antar da kuma cigaba da gudanar da ayyukanta.
Duk da karin ƙudin lantarki da aka yi wa kwastamomi da ke tsarin Band A, 'yan Nijeriyar na kokawa ganin cewa wutar ba ta waɗatar da su.
Amma Adelabu ya ce matakin na da muhimmanci wajen inganta tattalin arziki da cigaban ƙasar.
Wannan dai na nufin gwamnatin za ta kawo ƙarshen tsarin tallafin da ake bai wa ɓangaren lantarki, yanayin da zai tilasta ƙarin kuɗin wuta ga kowa.
No comments