Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Fara Kamen Mabarata da Almajirai A Abuja

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ɗauki matakin kama mabarata da ke gararamba cikin ƙwaryar birnin da kewaye. Ministan Abuja Nyesom Wik...


Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ɗauki matakin kama mabarata da ke gararamba cikin ƙwaryar birnin da kewaye.

Ministan Abuja Nyesom Wike ne ya bayar da umarnin yin kamen da kuma tayar da masu sayar da kayayyaki a wuraren da ba cikin kasuwa ba.

Hukumomi na cewa matakin zai kawar da yamutsi da kuma rashin tsari.

An bayyana atisayen mai taken 'Operation Sweep Abuja' a ranar Laraba a cikin wata sanarwa da Lere Olayinka, babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwar jama’a da kafafen sada zumunta ya fitar a madadin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Olayinka ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bisa umarnin Wike na kawar da Abuja da garuruwanta daga duk wani nau'i na tashin hankali, ciki har da ƙungiyar ƙwace ta "one chance".

No comments