Daga Zubairu Lawal, Lafia Shugabannin jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a mazabar Nasarawa ta Arewa sun bayyana amincewar su da Gwamn...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Shugabannin jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a mazabar Nasarawa ta Arewa sun bayyana amincewar su da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da ta Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule a matsayin Gwamnatin da takawo ci gaba.
Sun kuma tabbatar da cewa za su ba su Ęuri'a a zaben 2027, inda suka goyon bayan takarar shugaba Tinubu na sake maimata kujerar Shugabancin Ęasa a karo na biyu, da Gwamna Abdullahi Sule a matsayin kujerar Majalisar Dattawa a yankin Nasarawa ta Arewa.
Shugabannin Jami'iyyar ta APC da suka fito daga Ęananan Hukumomin Akwanga, Nasarawan Eggon da Wamba, l sun ce sun gamsu da mulkin Gwamna Abdullahi Sule da ya gudanar a jihar Nasarawa, saboda ya kawo zaman lafiya mai Éorewa da haÉin kan al'ummar jihar, ya kuma yi ayyuka a jihar Nasarawa da yankin Nasarawa ta Arewa.
Da yake Ęarin haske, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Timothy Anjide, ya ce wannan kira ne da gamayyar al'ummar yankin Nasarawa ta Arewa suka yi bayan haÉin gwiwa, inda masu ruwa da tsaki na APC suka sha alwashin ci gaba da goyon bayan manufofi Gwamnatin Abdullahi Sule da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’ummar yankin da jihar baki daya.
Ya kuma bayyana cikakken goyon bayan su ga burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a 2027, masu ruwa da tsakin sun yabawa Shugaban kasa bisa yadda ya naÉa ’ya’ya maza da mata daga yankin Nasarawa ta Arewa a manyan mukamai na hukumomin tarayya, kwamitoci da cibiyoyi.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na APC a yankin Nasarawa ta Arewa, Shugaban Ęaramar Hukumar Akwanga kuma Shugaban Ęungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta jihar Nasarawa (ALGON) , Hon. Safiyanu Isa Andaha ya ce taron an shirya shi ne domin tattauna hanyoyin ci gaba da Ęarfafa jam’iyyar da mambobinta a yankin.
Ya Ęara da cewa, “An cimma matsaya baki Éaya cewa Mai Girma Gwamna Abdullahi Sule ya kamata ya tsaya takarar Sanata a zaÉen 2027. Ina da tabbacin cewa gwamnan mu, wanda ya gaji tsarin DimokuraÉiyya, zai saurari muryar jama’ar sa ya amsa kiran mu.
“Baya ga amincewar da aka yi wa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Sule don zaÉen 2027, wani babban dalilin taron shi ne Ęarfafa haÉin kan jam’iyya. Mun yi magana da kan mu cewa domin ci gaban jam’iyyar, dole ne mu watsar da duk wata gaba ko sabani mu haÉa kai mu yi aiki tare a matsayin al’umma.”
No comments