Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomi Tudun Wada da Doguwa, Sardaunan ƙasar Hausa Hon. Alhasan Ado...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomi Tudun Wada da Doguwa, Sardaunan ƙasar Hausa Hon. Alhasan Ado Doguwa ya bayyana cewa a lokacin rayuwar Marigayi Alhaji Aminu DlƊantata, a duk lokacin suka haɗu da shi ya yi kan kira ga 'yan majalisa akan a riƙe haƙƙin mutane.
Hon. Alhasan ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Marigayin a lwanakin baya, inda ya zanta da Matattarar Labarai.
Hon. Alhasan ya ce kuma Marigayin yana nuna musu cewa su sani ɗan majalisa wakilin al'umma ne ,wanda duk Allah ya ba shi haƙƙin al'umma, to daidai yake da cewa kowanne mutum makiyayi ne, kuma Allah zai tambayi kowa akan abin da aka ba shi kiwo.
Hon. Alhassn Ado Doguwa ya ci gaba da cewa rashi ne babba aka yi na Aminu Ɗantata, wanda zai wuya a sami wanda zai cike gurbin sa da gaggawa. Ya ce, sai dai da yake Allah shi ne mai komai mai kowa, suna roƙon ya kawo wanda zai kwatanta irin abin da ya yi wa al'ummar Nijeriya, musamman musulunci.
No comments