Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba, Gusau A Kwanakin Baya Ne Ƙungiyar 'Sawabiqul Jiyadi' Taron Ta Gudanar Da Taron Ƙara Wa juna sani ga...
Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba, Gusau
A Kwanakin Baya Ne Ƙungiyar 'Sawabiqul Jiyadi' Taron Ta Gudanar Da Taron Ƙara Wa juna sani ga Malaman Makarantun Allo na Ƙaura-Namoda da kewaye na wuni biyu.
Wakilin Matattarar Labarai ya ruwaito mana cewa rana ta farko, Malam Falalu Mahi Kamarawa ne ya gabatar da ƙasida mai taken 'Rawar da Makarantun Allo ke takawa wajan kyautata tarbiyyar Al'umma.' Yayin da Sheikh Malam Junaidu Usman Limamin Masallacin Juma'a na Sheikh Isa Bini Ramadan Lugun Malamai ya yi mata ta'aliƙi.
Shi ma Malam Shehu Salisu Na 'yan Zikiri ya gabatar da tasa ƙasidar mai taken 'Tsarr-tsaren da Makarantun Allo ya kamata su bi wajen karbar Ɗalibai da samar masu da isasshen wurin kwana'.
Yayin da Farfesa Jafaru M. Kaura ya yi mata ta'aliƙi.
A rana ta biyu an gabatar da Maƙala ɗaya mai taken 'Samar Wa Ɗalibai hanyoyin Dogaro da kai,' wadda Malam Kabiru Usman Sama'ila (Dan-Kabi) ya gabatar. Yayin da Dakta Aminu Umar Gummi Sakataren zartarwa na hukumar bunƙasa ilimin harshen Larabci da addinin musulunci na jiha ya yi masa ta'aliƙi.
An karrama sama da mutane 400 da takardar shedar halartar taron da kuma wasu daga cikin waɗanda suke bai wa wannan ƙungiyar goyon baya da hadin kai.
Shi ma a nasa jawabi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Jalaluddeen Sambo ya yi Godiya ga dukkanin waɗannan suka halarci wannan taro, inda ya ce ayyukan wannan ƙungiya za su ci gaba a kowane yanki da ya shafi addini.
Ya ci gaba da cewa, wannan ƙungiya ta kafa makarantun addini masu yawan gaske, sannan dukan makarantun da ke wannan yanki na Islamiyya da Kulliya yana da wahala a rasa wakilan wannan ƙungiya daga cikin jagororin ta.
Ya ce wanna ƙungiya ba ta da alaƙa da kowane ɗan siyasa ko Gwamnati, kuma gudumawar su tana kaiwa har gidajen gyaran hali da asibitocin wannan yanki.
Manyan mutanen dama sun sami halarta a waɗannan ranaku, sun haɗa da Dr Yusuf Nasir Tsohon shugaban Makarantar Federal Polytechnic Ƙaura, Babban Limamin masallacin Juma'a na biyu Malam Badamasi Dalhatu, Khalifa Malam Maisuna na Malam Babba, Khalifa Malam Muhammad na Gangaren Makaranta, Khalifa Malam Sani Malam Mahi Kamarawa Babban Limamin masallacin Ƙadiriyya, Sakataren ilmi na Ƙaura Bashir Muhammad, Ibrahim Isah Daraktan Makarantun Allo na jaha, wakilin Uban ƙasar Barayar Zaki da dukkanin jagororin Kungiyar da 'yan kwamiti.
No comments