Daga Ibrahim Muhammad, Kano Majalisar Hafizan Alƙur'ani mai girma, ƙarƙashin jagorancin Garkuwan Hafizai Gwani Yusuf Hamza Yusuf (Abu ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Majalisar Hafizan Alƙur'ani mai girma, ƙarƙashin jagorancin Garkuwan Hafizai Gwani Yusuf Hamza Yusuf (Abu Abdulmajid) ta gudanar da saukar Alƙur'ani mai girma na adadin sauka mai yawa don sadaukar da ladan ga lMarigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Da yake zantawa da 'yan jarida bayan kammala addu'oil'in da ya jagoranta, Gwani Hamza Yusuf Hamza (Abu Abdulmajid ) ya ce sun ji wannan rashi a jikin su wanda ba a Kano kawai da Nijeriya aka yi wa ba, Duniya aka yi wa.
Ya ce gudumawar da ya bayar a Duniya ba za ta ƙirgu ba. Shi mutumin kirki ne mai ƙaunar Allah da Manzon sa, ya bayar da gudumawa ta kowane bangaren, harkar ilimi da lafiya da addini da kyautata zumunci. "Muna fatan Allah ya karbi ayyukan sa," in ji Abu Abdulmajid.
Shugaban mahaddatan ya ce, Duniya ma shaida ce cewa Alhaji Aminu Ɗantata mutumin kirki ne kuma Allah ya cika masa burin sa ,dama babban burin sa a binne shi a Madina birnin Annabi, kuma Allah ya cika masa buri. Kuma ya bar 'ya'ya masu albarka.
Daga nan ya yi kira ga al'ummar Musulmi akan su sani yin abu domin Allah irin yadda Aminu Ɗantata ya yi, su yi ƙoƙari su riƙa taimaka wa bayin Allah, domin shi dukiyar sa Allah ya sa mata albarka yana tsarkake ta.
Gwani Yusuf Hamza Yusuf (Abu Abdulmajid) Garkuwan Hafizai ya ce bai taba ganin mai arzikin da yake raye ba ya burin Allah ya ƙara masa lokaci ya ci gaba da rayuwa a Duniya ba, kamar Alhaji Aminu Ɗantata, ya shirya wa tafiya lahira kuma ya tafi a cikin aminci da yardar Allah.
No comments