Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Biya N20,000 A Matsayin Sadakin Jikar David Mark Domin Ragewa Matasa Tsoron Aure

An biya N20,000 ga iyalan Honarabul Blessing Onuh da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini a jihar Benuwe a matsayin sadakin auren É—iyarta. Hon...


An biya N20,000 ga iyalan Honarabul Blessing Onuh da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini a jihar Benuwe a matsayin sadakin auren É—iyarta.

Honarabul Onuh É—iya ce ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban sabuwar jam'iyyar haÉ—aka ta ADC, Sanata David Mark.

Adadin kuÉ—in ya zama sadakin auren jikar Mark kuma iyalan Farfesa Bishop Obeka Sunday, Shugaban Jami’ar Wesley da ke jihar Ondo ne suka biya.

Farfesa Sunday shi ne mahaifin Caleb Obeka, wanda ya auri Margaret Onuh bisa ga al'ada. Kuma ma'auratan su na da digiri da PhD.

Basaraken gargajiya, Ochi Otukpo, Dokta John Eyimonye ne ya jagoranci É—aurin auren, inda ya bayyana cewa Allah ne ya maddara auren. Ya bayar da shawarar a rage farashin sadakin dominarfafa wa matasa gwiwa wajen yin aure, tare da bayyana cewa babban abin da ya shafi auratayya shi ne samun albarkar Ubangiji.

Dokta Eyimonye ya gode wa iyalan Onuh da suka amince da sadakin amaryar, inda ya ce muhimmancin shi ne na ba da misali mai kyau ga wasu.

Da yake jawabi a madadin iyalan Onuh, Mista Ahubi Jonathan ya bayyana cewa bai kamata sadaki amaryar ya yi yawa ba, ya Æ™ara da cewa ma’auratan su na buÆ™atar tallafi don samun ci gaba a rayuwar aurensu da kuma rayuwa cikin jin daÉ—i.

Ya ce ya kamata a daina kashe maqudan kuɗi a wajen sadaki a masar Idoma domin ƙarfafa gwiwar matasa su yi aure.

Farfesa Sunday ya nuna godiya ga Hon. Iyalan Onuh saboda fahimtarsu wajen karbar sadakin amaryar.

No comments