Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da korar wani ɗan ƙasar Amurka, Alex Barbir, bisa zargin yin kalaman tunzura jama’a da za su iya haddasa tashi...
Babbar Mataimakiya Ta Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan Harkokin Hulɗa da Al’umma (shiyyar Arewa ta Tsakiya), Abiodun Essiet, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin. Ta bayyana cewa ayyukan Barber sun zama babbar barazana ga haɗin kan ƙasa.
“Haka ne, mun fahimci abubuwan da Alex Barbir yake ƙullawa, don haka ya kamata in sanar da ku cewa Alex Barbir ba ya Najeriya a halin yanzu,” in ji Essiet.
“An kore shi, za mu iya cewa an fitar da shi daga ƙasar ne saboda ayyukan rarraba kawuna da yake yi.”
Ta yi zargin cewa kalaman na Barber sun haifar da mummunan sakamako, inda ta alaƙanta jawabin da ya yi a birnin Jos da wasu tashe-tashen hankula da suka biyo baya.
A cewarta: “Nan take bayan ya yi jawabin nasa a Jos, mutane da dama ba su sani ba cewa an kashe Musulmai mutum biyu jim kaɗan bayan jawabin nasa. Saboda tasirin kalaman tunzura jama’a da yake yi ne aka fitar da shi daga ƙasar.”
Essiet ta jaddada cewa gwamnati ta ɗauki matakin ne domin kauce wa maimaita irin munanan abubuwan da suka faru a tarihi sakamakon kalaman rarraba kawuna.
Ta buga misali da kisan kiyashin da ya faru a ƙasar Rwanda a shekarar 1994, inda ta ce: “Na je Rwanda sau da dama; na ziyarci wurin tunawa da kisan kiyashin Rwanda. Abin da Alex Barbir yake faɗa kusan iri ɗaya ne da abin da wasu ‘yan waje suka yi a Rwanda, inda suka raba kan kabilun Hutu da Tutsi, wanda hakan ya kai ga kisan kiyashi.”
Mataimakiyar shugaban ƙasar ta yi gargaɗin cewa kada a bar irin waɗannan kalamai su yi tasiri a Najeriya, tana mai cewa: “Bisa ga abubuwan da muka sani, ba ma son Najeriya ta bi wannan hanyar, domin ba za ta taimaki kowa ba. Kada mu bar mutanen da ba su san tarihin rikice-rikicenmu ba su raba mu.”
Daga ƙarshe, ta jaddada mahimmancin haɗin kai da kuma ɗaukar nauyin magance matsalolin tsaro na ƙasa baki ɗaya, inda ta yi kira da a ɗauki kwararan matakai na soja kan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai.

No comments