Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NELFUND: An Fara Biyan Kuɗin Kashewa Na Ɗaliban Da Suka Gyara Asusun Bankin Su

Hukumar Lamunin Karatu ta Najeriya (NELFUND) ta fara biyan kudin kashewa na buƙatun yau da kullum ga daliban da suka sabunta bayanan asusun ...




Hukumar Lamunin Karatu ta Najeriya (NELFUND) ta fara biyan kudin kashewa na buƙatun yau da kullum ga daliban da suka sabunta bayanan asusun bankinsu daga kananan asusu (Wallet) zuwa manyan asusun bankuna. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktar Sadarwa ta NELFUND, Mrs Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar a Abuja, inda ta bayyana cewa matakin ya kawo karshen tsaikon da aka samu wajen biyan kudin.

Fiye da dalibai 3,600 da suka yi rajista da kananan bankuna ta ‘Wallet’ ne suka samu kudin su da ya makale bayan da suka sabunta bayanansu a shafin NELFUND zuwa babban asusun bankin kasuwanci. Oluwatuyi ta yaba da hakurin daliban da suka fuskanci jinkirin, tana mai cewa hadin kansu da jajircewarsu ne suka sa aka samu wannan nasarar.

Ta bukaci wadanda ba su sabunta bayanansu ba su tura korafi ta hanyar shafin NELFUND ko su kai rahoto ga ofishin fasahar sadarwa (IT) na makarantar su domin a tura bukatunsu zuwa hukumar. Oluwatuyi ta kuma bukaci dalibai su yi amfani da shafukan hukuma kawai wajen tuntuɓar NELFUND, da kuma taimakawa abokan su da ke bukatar ƙarin haske.
 

No comments