Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana damuwa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka juya maganganun Sanata Kashim Shettima da ya gab...
Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana damuwa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka juya maganganun Sanata Kashim Shettima da ya gabatar a lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” a Abuja, ranar Alhamis.
Sanarwar wacca mai ba shi shawara kan harkokin labarai Stanley Nkwocha ya fitar ta bayyana cewa jawabin Shettima na nuni ne zuwa ga tsohon tarihin matsalolin da ya fuskanta a lokacin yana Gwamnan Borno sakamakon rikicin Boko Haram, ba wai yana tsokaci ne kan abubuwan da ke faruwa a Jihar Rivers ba.
Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa, Shettima ya yi amfani da misalan tarihi ne don yaba wa marubucin littafin, Mohammed Bello Adoke (SAN), bisa jajircewarsa a lokacin da yake Ministan Shari’a.
Ofishin ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga muƙaminsa ba, sai dai an dakatar da shi ne bisa matakin doka domin dawo da doka da oda a Jihar Rivers. An ɗauki matakin ne bisa tanadin Sashe na 305 na kundin tsarin mulki, tare da amincewar majalisar dokoki ta kasa.
A ƙarshe, Sanarwar ta bayyana cewa duk wani yunƙurin juya kalaman Shettima a matsayin suka ga gwamnatin yanzu ko wata alama ta rikici tsakanin manyan jami’an gwamnati, labari ne na ƙarya da ƙoƙarin kawo rashin zaman lafiya.
Ofishin ya jaddada cewa Shettima da Tinubu suna aiki tare domin kare Dimokuraɗiyya da doka a Nijeriya.
No comments