A halin da ake ciki dai, majalisar Malamai a ƙarƙashin Ƙungiyar Ɗariƙu ta jihar Kano ta musanta rahoton da ke cewa an gudanar da zaman tat...
A cikin wata sanarwa da Majalisar ta fitar, wanda kuma ɗauke a shafin ta na facebook, ta bayyana cewar ba ta da masaniya akan wancan zaman da 'yan sanda ke iƙirarin an gudanar da shi, kuma ba ta da wakili a wannan zaman. Haka kuma, Majalisar ta ce a halin yanzu tana da nata koken da tuni ta shigar a hukumance kan kalaman da ake zargin Lawal Triumph ya yi na raina girman Annabi (S.A.W) ta hanyar jingina shi S.A.W da ƙwarƙwata, wanda suka bayyana wannan a matsayin abin kunya da takaici ga duk wani musulmin da ya san darajar Ma'aiki S.
"Wannan magana ce mai matuƙar muni da raini ga Manzon Allah (S.A.W). Don haka muna kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace akan gaskiya da kwatanta adalci, ba tare da nuna son kai ko bangaranci ba."
Haka kuma, Majalisar ta tuna da wani lamari makamancin wannan wanda ya faru da wani Malami daga kungiyar Izala, Baffa Hotoro, wanda shi ma ake zargin ya yi kalaman su’ul adab ga Manzon Allah (S.A.W).
A wancan lokaci, Kwamishinan Shari'a na jihar Kano ne ya bada umarnin a cafke shi, kuma aka tsare shi a ofishin 'yan sanda kafin fara shari’a da shi, daga bisani aka zargi wasu jami’an ‘yan sanda da haɗa baki aka ba da shi beli cikin Sirri, wanda hakan ya ba shi damar tserewa zuwa ƙasar Saudiyya," in ji Majalisar.
Don haka ta bayyana cewa irin waɗannan abubuwa na janyo shakku da rashin amincewa daga al’umma ga Hukumar 'Yan Sanda ta jihar Kano, musamman inda ake zargin su da nuna son kai ko kuma daukar bangare a cikin al’amuran da suka shafi addini da kare mutuncin Annabi Muhammad (S.A.W).
A ƙarshe, Majalisar ta yi kira ga ɗaukacin al’umma da su zauna lafiya, su jajirce wajen kare mutuncin Manzon Allah (S.A.W) ta hanyar nuna halin Dattako tare da tsayawa akan gaskiya sannan su ci gaba da bin doka. Ta kuma buƙaci hukumomin tsaro da su yi aikin su cikin kwatanta adalci da yin biyayya ga dokokin tsarin shari’a ba tare da nuna son kai ba.
No comments