Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗan Bello Ya Kubuta Daga Hannun DSS Bayan Kama Shi A Kano

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta saki shahararren ɗan sociyal midiya, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano. ...


Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta saki shahararren ɗan sociyal midiya, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano.

Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke.

Saukar matashin da ke zaune a ƙasar Chana a Nijeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi.

Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu.

Bayan nan ne Ɗan Bello ya wallafa hotonsa da tare da matashin lauya ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima a cikin mota.

A ƙarƙashin hoton da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kuma ya rubuta, “Masha Allah, kowa ya bar gida.”

Kawo yanzu dai babu bayani daga hukumomin tsaro ko Ɗan Bello game da dalilin tsarewar da aka yi masa da kuma abin da ya wakana tsakaninsu.

Ɗan Bello dai ya yi ƙaurin suna wajen yin bidiyon barkwanci kan matsalolin shugabanci da cin hanci a Nijeriya.

A baya-bayan nan sakonni da ya wallafa kan matsalar fanshon ’yan sanda da ta matsalar albashin malaman jami’a sun ɗauki hankali matuƙa.

No comments