Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Zamfara Ya Ƙudiri Aniyar Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta

 Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Gwamn...


 Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Gwamnan ya ƙaddamar da shirin Ciyar da Ɗaliban Makaranta ta Jihar Zamfara ranar Alhamis a makarantar firamare ta Dan-turai da ke Gusau, babban birnin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa shirin ciyar da ɗaliban makarantar zai baiwa ɗalibai damar shiga, nutsuwa, riƙewa, kammala karatu da kuma komawa zuwa manyan matakan ilimi.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara.

Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da rugujewar sassan ilimi da samar da haɗin gwiwa, kamar Bankin Duniya ta hanyar shirin AGILE da kuma UNICEF. A kwanakin baya Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha tare da haɗin gwiwar UNICEF, sun kafa wani kwamitin fasaha na shugabannin hukumomin da masu ruwa da tsaki domin ziyartar mananan hukumomi 14, da tantance yaran da ba su zuwa makaranta, da kuma tabbatar da shigar su makarantu.

“Shirin ciyar da ɗalibai a makarantu da muke ƙaddamarwa a yau, wani bangare ne na shirye-shiryen bayar da agajin gaggawa na inganta rajista da kuma riƙe ɗalibai a makarantu tare da yaƙi da yunwa da rashin abinci mai gina jiki. Wannan baya ga ƙoƙarin mu da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, Cibiyar Ci Gaban Tattalin Arziki ta Ƙasa da Ƙasa da Gidauniyar FINPACT, waɗanda suka amince da tallafa wa gwamnati wajen aiwatar da shirin domin yin aiki a matsayin tushen ilimi.

“A cikin sharuɗɗan, gidauniyar FINPACT za ta ɗauki nauyin ciyar da ɗalibai 1000 a Gusau, Maru, Anka, da Talatar Mafara, yayin da Cibiyar Raya Tattalin Arziki ta Duniya ke ɗaukar nauyin ciyar da ɗalibai 3300 a faɗin Gusau, Talatar Mafara, da Shinkafi.

“Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da sauran hukumomin bayar da agaji da su ƙara binciko hanyoyin samar da ƙarin ayyuka da shirye-shirye, wanda ba wai kawai hakan zai ƙara ƙaimi wajen samar da ilimi mai inganci ba ne, amma zai rage adadin yaran da ba su zuwa makaranta, ta yadda tare za mu mai da jiharmu ta zama abin koyi.”

No comments