Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa Miliyan 7 Za Su Amfana Da Horo A Fannin Fasahar Zamani Daga Gwamnatin Tarayya

A wani gagarumin mataki da zai canza rayuwar matasa a Nijeriya, Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniya da Hadaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) w...


A wani gagarumin mataki da zai canza rayuwar matasa a Nijeriya, Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniya da Hadaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wato Dubai domin horas da matasan Nijeriya fiye da miliyan bakwai a fannin fasahar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, da kasuwanci.

Yarjejeniyar ta samu ne yayin wata ziyarar manyan jami’an Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Cigaban Matasa, Ayodele Olawande, zuwa ƙasar Dubai, inda suka gana da cibiyar ƙirƙira ta Sharjah (Sharjah Entrepreneurship Centre – Sheraa).

A cewar Minista Olawande, “Shirin Nigerian Youth Academy (NiYA) zai ba matasa fiye da miliyan bakwai horo a fannin ilimin zamani, shugabanci, da ƙwarewar a bangaren sana’a.

“Muna fatan ganin matasan Najeriya sun koma masu ƙirƙira a duniya, ba kawai masu amfani da fasaha ba.” Inji shi

Haka kuma, an tattauna da Ministan Fasahar Wutar Lantarki, Tattalin Arzikin na Dubai, Omar Al Olama, kan yiwuwar haɗin gwiwa a fannin Artificial Intelligence (AI), kirkire-kirkire, da dabarun aiki daga gida.

A halin yanzu, shirin NiYA ya riga ya ɗauki matasa sama da 210,000, kuma yana fadada ayyukansa ta hanyar kafa cibiyoyin Greenhouse Centres a kowanne daga cikin ƙananan hukumomi 774 na Najeriya, domin bunƙasa ilimin zamani da kasuwanci daga tushe. A shekara mai zuwa (Satumba 2025), Najeriya za ta karɓi bakuncin taron National Digital Innovation Showcase, wanda GITEX ke daukar nauyi, domin nuna fitattun kamfanonin matasa 300 a fannin fasahar zamani tare da jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.

Wannan yunkuri yana da nufin haɗa Najeriya da manyan dandalin kirkire-kirkire na duniya kamar GITEX Africa, kuma ya dace da shirin Sabunta fata na Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ke da burin farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar amfani da fasahar zamani.
 

No comments