Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki A Saint Lucia Da Brazil

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Abuja daga ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saint Lucia da Brazil. Jirgin shugaban ƙasa ya sauka...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Abuja daga ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saint Lucia da Brazil. Jirgin shugaban ƙasa ya sauka a sashin shugaban ƙasa na Filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 1:30 na safe a ranar Lahadi.

Manyan jami’an gwamnati ne suka tarɓe shi, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Ƙasa da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da Ministan Harkokin Tsaron Cikin Gida, Bello Matawalle. Sauran da suka tarbe shi sun haɗa da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, Alhaji Ibrahim Masari, da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Tinubu ya bar Abuja ne a ranar 28 ga watan Yuni domin halartar wasu muhimman taruka na diflomasiyya a yankin Caribbean da Kudancin Amurka. Ziyara ta farko ta Shugaban Ƙasa ita ce zuwa ƙasar Saint Lucia inda ya gana da shugabannin ƙasashen Caribbean domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Kudancin duniya da na Caribbean (South-South Cooperation).

Daga nan ne ya wuce ƙasar Brazil domin halartar Taron Ƙungiyar BRICS na shekarar 2025 wanda aka gudanar daga 6 zuwa 7 ga watan Yuli. A gefen taron, Tinubu ya gana da Shugaban Ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, inda suka tattauna batutuwa masu alaƙa da faɗaɗa cinikayya, samar da kuɗin ayyukan gina ababen more rayuwa da kuma zurfafa alaƙar bunƙasa al’adu tsakanin ƙasashen biyu.
 

No comments