Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RASUWAR BUHARI: Shugaba Tinubu Ya Tura Shettima Zuwa Ladan Don Tahowa Da Gawar

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tura mataimakin sa, Kashin Shettima zuwa Landan don tawowa da gawar tsohon shugabn ƙasa Muhammadu Buhari,...


Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tura mataimakin sa, Kashin Shettima zuwa Landan don tawowa da gawar tsohon shugabn ƙasa Muhammadu Buhari, wanda Allah ya yi wa rasuwa yau Lahadin nan a wani asibiti da ke birnin Landan ta ƙasar Ingila.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yayun Shugaban ƙasan, Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne yau ɗin da misalin ƙarfe 4.30 bayan rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya yi magana da matar tsohon shugaban ƙasan, Aisha, inda ya miƙa saƙon ta'aziyyar sa.

Daga nan ne shugaba Tinubu ya bayar da umurni ga matamakin sa Kashin Shettima ya wuce Ingilar domin tahowa da gawar ta Muhammadu Buhari.

A ƙarshe shugaba Tinubu ya bayar da umurnin a sauko da tutar Nijeriya ƙasa-ƙasa don girmamawa ga Tsohon shugaban.
 

No comments