Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Yaba Wa Hon. Garba Diso Wajen Tallafa Wa Ci Gaban Ilimi -Gaddafi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukuma Gwale ta jihar Kano, Hon. Garba Ibrahim Dis...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukuma Gwale ta jihar Kano, Hon. Garba Ibrahim Diso ya yi abubuwa na tallafa wa al'ummar mazaɓar sa, musamman harkar bunƙasa ci gaban ilimi a zuwan sa majalisa cikin ɗan taƙaitaccen lokaci.

Injiniya Gaddafi Sani Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida a wani taro da jami'ar Yusuf Maitama ta shirya, inda ya wakilci ɗan Majalisar.

Ya ce, cikin abubuwa da ya yi na tallafin ilimi, sun haɗa da bayar da fom na jarabawar JAMB kyauta, da na NECO. Da horar da matasa dabarun zamani na yin takalma da abubuwa na wayar da kan jama'a akan manufar aikin Ɗan majalisa.

Injiniya Dakta Gaddafi Sani Shehu ya bayyana cewa taron ya yi armashi, duba da yadda Shehunan Malamai suka gabatar da bayanai akan ci gaban adabin Hausa da rubuce-rubuce, wanda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya gabatar, da kuma muƙala da Farfesa Kamilu Sani Fagge ya gabatar akan ci gaban kasuwanci da ci gaba da aka samu.

Injiniya Dakta Gaddafi Sani Shehu ya ce, Jami'ar Yusuf Maitama ta yi ƙokari a wannan lokaci da sababbin abubuwa na ɗabi'u da suke shigowa ta ɓangaren ci gaban al'umma ya suka ga dacewar a kira wannan taro a tattauna, a bayar da shawarwari.

 

No comments