Daga Ibrahim Muhammad, Kano An buɗe ofishin Hukumar tsaro ta Cicil Defence (NSCDC), wacce Ƙungiyar 'yan kasuwar Galadima ta Kano suka s...
An buɗe ofishin Hukumar tsaro ta Cicil Defence (NSCDC), wacce Ƙungiyar 'yan kasuwar Galadima ta Kano suka samar a harabar kasuwar domin inganta tsaro.
A taron buɗe ofishin, Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano, Hon. Abbas Sani Abbas ya bayyana matuƙar jin daɗinsa bisa ƙoƙarin 'yan kasuwar na Galadima da Manajan Darakta na Hukumar kasuwar Muhammad Abubakar Rimi akan samar da ofishin.
Ya yi nuni da cewa tsaro abu ne muhimmi ga ci gaban jihar Kano da ƙasa don haɓakar harkar Kasuwanc, za su kuma cigaba da bada kulawa damin inganta harkar tsaro a dukkan kasuwannin Jihar Kano domin masu saye da sayarwar su yi harkokinsu a cikin aminci.
Abbas Sani Abbas ya kuma yaba da irin haɗin kai da goyon bayan da Hukumar NSCDC suke ba su a Jihar Kano, inda ya ce za su ci gaba da haɗa kai da su da sauran hukumomi na tsaro don samar da tsaro a kasuwanni.
Tun da farko a jawabin s, Manajan Daraktan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, Alhaji Abdul Bashir Hassan ya bayyana mutuƙar farin ciki da buɗe ofishin na Hukumar tsaron don bunƙasa tsaro, wanda ya ce, ma akwai ofishin yan sanda a kasuwar.
Abdul Bashir Hassan ya ce, Hukumar kasuwar Abubakar Rimi Galadima da Singa za ta sanya kayan aiki ga ofishin tsaron na NSCDC da aka samar domin zai taimaka wa jami'anta wajen aikinsu.
Shi ma a jawabinsa, wakilin Kwamandan Hukumar tsaro masu kula da fararen hula na jihar Kano, ACC Musa Usman ya bayyanna jin daɗinsa bisa samar musu da ofishin domin bada tsaro. Yana mai cewa, za su ci gaba da bada haɗin kai domin inganta tsaro da suke yi a kullum na awa 24.
Musa Usman ya ce dama suna da babban ofishinsu na Ƙaramar Hukumar Fagge a ƙarƙashin jagorancin Kwamandan, Hajiya Amina, wanda kuma ofishin kasuwar da aka buɗe zai zama kasance a ƙarƙashin kulawar su ne.
A jawabin sa shugaban haɗɗiyar ƙungiyar 'yan Kasuwar Galadim, Alhaji Mustapha Shu'aibu Sulaiman ya ce taron buɗe ofishin na jami'an tsaro na Civil defence da suka samar rana ce ta tarihi gare su, musamman saboda zuwan Kwamishinan Kasuwanci.
Ya yi nuni da cewa Abbas Abdullahi Abbas Kwamishinan Kasuwanci na Kano kullum ƙoƙarinsa ya ɗora 'yan kasuwa a harkar Kasuwanci na zaman, wacce ta bijiro da sabbin tsare-tsare ga 'yan kasuwa daidai da tafiyar zamani.
Ya kara da cewa baiwa dan kasuwa Kwamishinan Kasuwanci a Jihar Kano da Kuma nada manajan daraktan kasuwar Sabon gari da dukkansu Yan kasuwa ne abune da zai taimaka wajen bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano.
Alhaji Mustapha Shu'aibu ya ce kyakkyawan jagoranci na Kwamishinan Kasuwanci na jihar Kano, Hon.Abbas Sani Abbas da Manajan Daraktan kasuwar Sabon Gari, Hon. Abdul Bashir Hassan ne suka taimaka wajen jawo nasarar samar da ofishin a wannan kasuwa ta Galadima.
Bayan buɗe ofishin da Kwamishinan Kasuwanci, Hon Abbas Sani Abbas ya jagaranta, ƙungiyar ta kasuwar Galadima, ƙarƙashin shugaban ta,
Alhaji Mustapha Shu'aibu Sulaiman sun miƙa masa kyauta ta musamman da suka bai wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf saboda yaba wa da irin gudumawar da ya ke bayarwa ga ci gaban Kasuwanci a Jihar Kano
No comments