Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa 'Yan Jihar Kano Mazauna Kudancin Nijeriya Sun Yaba Wa Sarkin Kano

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna A wani zama na musamman da ƙungiyar matasa ƙwararru 'yan asalin jihar Kano, mai suna Kano Youth Profession...

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

A wani zama na musamman da ƙungiyar matasa ƙwararru 'yan asalin jihar Kano, mai suna Kano Youth Professionals, mazauna Kudancin Nijeriya da kuma Arewa ta Tsakiya suka gudanar a Kaduna a cikin makon nan, sun yaba matuƙa da yadda Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yake tafiyar da mulkinsa, musamman wajen yadda yake nuna tausayi ga al'ummar sa da jama'ar ƙasa gaba ɗaya.

A wata takardar bayan taro da shugannin ƙungiyar na Kudu da na Arewa ta Tsakiya, Mansur Sulaiman da Bashir Sa'ad su ka sa wa hannu, sun ce "Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kullum ya na nuna halin dattako da tausayi wajen tafiyar da mulkinsa.

"Mun ji daɗi matuƙar gaske tayadda mu ka ga ya yi kira ga 'yan kasuwa da su sassauta farashin kayan abinci, da ƙara kira ga masu hannu da shuni su taimaka wa talakaw, musamman ganin yadda wata mai alfarma na Ramadan ya kusanto." 

Su ka ci gaba da cewa sun ji daɗin ganin yadda Sarkin ya yi kira ga gwamnatin tarayya, ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu da ta ƙara duba wahalar da talakawa ke ciki na fatara da yunwa. Ya yi kiran ne lokacin da uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta kai wata ziyara fadar Sarkin a kwana nan. 

Matasan sun kuma yaba da wasu 'yan gyare-gyare da su ka ce gwamnatin tarayyar ta fara. Su ka ce, "Irin waɗannan abubuwan alheri na Sarkin Kano su na sa wa mu na tunawa da Marigayi, Mai Martaba Ado Bayero."

Ganin irin hoɓɓasar da Sarkin ke yi wajen roƙon shugannin ƙasa da a fito da wasu manufofi don inganta rayuwar al'umma, 'matasan sun roƙi gwamnatin tarayya da ta haɗa hannu da Sarakuna wajen ƙara wayar da kan al'umma ga da tsare-tsaren gyaran ƙasa da gwamnatin ke yi. 

Suka ce, shi Mai Martaba kullum zancen sa ɗaya ne, wato ta yaya talaka zai samu sararawa a rayuwa. Kullum abin da ya sa a gaba shi ne ya ba shugabanni shawara bisa girmama jun, saboda a sauƙaƙa rayuwa da halin ƙaƙa-ni-ka-yi da jama'a ke ciki," in ji takardar.

No comments