Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sace 'Yan Firamare Ya Tada Hankalin Al'ummar Kaduna

-Ƙungiyar Shgabannin Jam'iyyun Siyasa Na Arewa Sun Yi Allah-wadai Daga Musa Muhammad A 'yan kwanakin nan ne aka sace wasu ɗaliban ma...

-Ƙungiyar Shgabannin Jam'iyyun Siyasa Na Arewa Sun Yi Allah-wadai

Daga Musa Muhammad

A 'yan kwanakin nan ne aka sace wasu ɗaliban makarantar Firamare da na Sakandare sama da 100 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. 

Kawo yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka saceba, amma mazauna yankin sun ce sama da yara 100 ne.

Rahotanni sun ce shugaban makarantar da wasu ma’aikatan makarantar na cikin waɗanda abin ya shafa.

Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasar Arewa ta miƙa saƙon jajen ta. Babban Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Malam Mikailu Abubakar a cikin wata sanarwar manema labarai a jiya 7 ga Maris, 2024 ya ce: "Wannan ɗanyen aikin na garkuwa da yaran da ba su ji ba ba su gani ba, daga makarantarsu, ya jefa al’ummar Kuriga da ma sauran al’umma cikin matuƙar kaɗuwa."

"Sace waɗannan ƙananan yara ɗalibai na nuni da mummunan hari a kan haƙƙin ilimi da kare lafiyar yaranmu. Ya zama cin fuska ga kimar zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban da muke da shi a matsayinmu na kasa. Muna Allah wadai da wannan ta'addanci da kakkausar murya tare da yin kira da a gaggauta ɗaukar matakin hukunta waɗanda suka aikata laifin," in ji sanarwar.

Daga nan Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da jami’an tsaro da abin ya shafa da su ba da fifiko kan aikin ceto tare da ɗaukar dukkan matakan da suka dace don ganin an dawo da ɗaliban da aka sace ga iyayen su cikin ƙoshin lafiya. Dole ne a haɗa ƙarfi da ƙarfe don gaggauta sakin su tare da rage raɗaɗin iyeyen waɗanda abin ya shafa.

Sanarwar ta ce, "Sannan muna kira ga gwamnati da ta aiwatar da tsauraran matakan tsaro a fadin cibiyoyin ilimi a jihar Kaduna da ma yankin Arewa baki ɗaya, domin hana afkuwar irin wannan munanan lamari a nan gaba".

"A matsayinmu na wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban na yankin Arewa, muna kara jaddada ƙudurinmu na haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin rashin tsaro da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummarmu.

"Muna kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su hada kai domin yaƙar wannan annoba ta garkuwa da mutane da tashe-tashen hankula, da kuma kokarin samar da makoma mai inganci da wadata ga al’ummarmu."

Matattarar Labarai ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe a lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) na ranar Alhamis.

Ɗaliban sakandare sun koma ginin makarantar da ke cikin garin Kuriga a shekarun baya saboda rashin tsaro, inda suka yi watsi da tsohon ginin makarantar da ke wajen garin.

Wani mazaunin garin Shitu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce galibin ɗaliban sun tsere daga ajijjuwan su a lokacin da suka hango ’yan bindigar a harabar makarantar.

Shi ma wani mazaunin garin Lawal Kuriga ya shaida wa manema laabarai cewa an garzaya da waɗanda aka sace zuwa cikin dajin.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar domin kwamishinan sa ido na ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, bai mayar da martani kan sakon da aka aike masa ba.

An kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ta wayar tarho kuma har yanzu bai amsa wani saƙo da aka aike masa ba.

 

No comments