Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar ƙirƙire-ƙirƙire da koyon sana'o'i da ke ƙarƙashin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Makarantar ƙirƙire-ƙirƙire da koyon sana'o'i da ke ƙarƙashin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta gudanar bukin yaye ɗalibai a karon farko na makarantar.
A wata zantawa da manem labarai, Daraktan makarantar, Injiniya Auwalu Sanusi ya bayyana cewa, taron na haɗin gwiwar yaye ɗaliban ne na Shekaru 11, domin ba a taɓa taron yaye ɗalibai makamancin wannan ba tun aka kafa ta.
Ya ce, tsarin ɗaukar ɗalibai da yaye su yana cikin tsari na karatunsu da Hukumar MBT ta sahalle a riƙa yaye ɗalibai, shi ya sa yanzu suka haɗa da waɗanda suka gama shekara 10 da na huɗu da na biya, wanda yin irin wannan taro yakan daɗa farfaɗo da zumunci a tsakanin ɗalibai saboda wani ya daɗe bai ga ɗan uwan sa ba, amma dalilan taron sun gamu.
Injiniya Auwalu Sanusi ya ce, an yaye ɗalibai 1,100,00 daga 'yan aji na 2011 zuwa 2024, wanda suka fito daga fannoni huɗu na darussan da ake da suka haɗa da "Telecomucation technology Networking and security system, Software Engineering, Hardware Technology."
Ya ci gaba da cewa, makaranta ce da ɗalibi zai iya dogaro da kan sa, duk abin da ake koya musu mafi yawa a aikace n, kuma in yaro ya gama zai samu shaida, wanda ko bai sami aiki ba, zai iya riƙe kansa da fasahar da ya koya.
Ya ƙara da cewa, akwai kuma harkar bankin musulunci, kamar yadda su ka yi hasashe cewa abu ne da ya shafi musulunc, dalibi zai iya yin abin da ya shafi rabon Gado, sannan zai iya aiki a bankuna da ba sa harka da kuɗin ruwa.
Daraktan ya ce Hukumar da ta sahalle a riƙa wannan darasi, ta ɓullo da tsari cewa makarantu irin wanɗannan, za su koma masu cin gashin kan su kafin shekarar 2027.
Daga nan sai Injiniya Auwalu Sanusi ya roƙi gwamnatin jihar Kano, kamar yadda NBT ta fitar da tsarin suna fata za a ɗauki mataki domin cika ƙa'ida ba sa son su ga har lokacin ya zo ba a cimma abin da aka ba su ƙa'ida akai ba.
No comments