Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Komawar Kasuwar Magunguna Zuwa Ɗangwauro Zai Kawar Da Yaɗuwar Jabun magunguna -Shugaba Husaini

Komawar Kasuwar Magunguna Zuwa Ɗangwauro Zai Kawar Da Yaɗuwar Jabun magunguna  -Shugaba Husaini Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban Kasuwar...

Komawar Kasuwar Magunguna Zuwa Ɗangwauro Zai Kawar Da Yaɗuwar Jabun magunguna  -Shugaba Husaini

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Kasuwar masu sayar da magunguna na Kanawa ta Ɗangwauro "Kanawa Pharmaceutical Partners",  Alhaji Hussain Labaran Zakari ya bayyana cewa nasarar da aka samu na tarewa da masu sayar da magunguna ke yi a halin yanzu, ba nasu ba ne su kaɗai, ta masu sayen magani ne domin su ne suka fi muhimnanci fiye da kowa, kuma tattare su a wurin zai taimaka wajen rage yaɗuwar jabun magungunan.

Alhaji Husaini ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da 'yan jarida a Kano, inda ya ce, idan akwai masu sayar da magani 1000 a Kano, to masu sha sun fi 10,000,000, don haka amfanin tsarkake harkar zai koma ne ga jama'a, waɗanda Likita ke sawa su sha maganin wata larura. 

Ya ci gaba da bayyana cewa, kuma hakan zai  amfanin dukkan al'umma da suke koke-koke na cewa ana sayar da magunguna masu cutar da rayuwa da ke jawo aikata laifuka, zai kuma rage cutar da matasa da ake yi da miyagun ƙwayoyi, zai kuma taimaka wa  mutanen gari da hukumomi  da suke ƙoƙarin hana laifuka.

Daga nan sai Alhaji Husaini Zakari ya yi nuni da cewa waɗanda suka turje ga ƙin yarda da kasuwar da farko wasu sun yi ne saboda hali na sabo da inda suke sana'a a da, domin wani idan ya saba da wuri, sai ya ga ba ya son bari, ko kuma  yana tsoron inda zai koma akan karɓuwar harkar da yake. 

To, amma sai dai Shugaba Husaini ya ce, a tarihin Kano an tashi masu harkokin sana'a daban-daban   an sauya musu wuri, yanzu inda suka koma ya haɓaka, irin su kasuwar hatsi ta Dawanau, da Kasuwar Ƙofar Wambai, masu sayar da Bulawus da dai sauran su da yawa, duk yanzu suna murna da komawa inda aka kai su.

Ya ƙara nuni da cewa wasu kuma suna tsoro ne cewa irin sana'ar da suke ba ta dace da inda za su koma ba, wasu su ce wurin ya yi musu nisa. Saboda haka ya ce, su abin da suke fata a matsayin su na masu harkar sayar da magani,abin zai zama alkhairi ga wanda yake so ya koma  da wanda ba ya so sai dai hukuma ta matsanta masa.

Alhaji Hussain Labaran Zakari  ya ce yanayin hada-hadar kasuwar, da an soma da mutane kaɗan, amma yanzu kullum mutane suna zuwa, masu sayen shago da masu kama rumfunan haya da masu sayan magunguna, kullum dai a cike take.

Ya ce ita kasuwar an yi ta ne saboda masu zuwa su sari magane  ƙwararru su kai wajen sayar da magani daidai da tsarin dokaa riƙa saye idan likita ya yi umurni.

Daga nan sai Alhaji  Husaini ya gode wa al'umma da suka fahimci manufar samar da Kasuwar magani a Dangwauro suka gane cewa nan ne wajen da hukuma ta amince a yi hada-hadar magunguna cikin tsari na doka da Asibitoci da hukumomi za su riƙa zuwa su saya.

Husaini labaran zakari ya kuma gode wa gwamnatoci na baya da na yanzu da suka bada gudummuwa domin nasarar da suka samu, musamman a wannan lokaci na  Kwamishinan lafiya na Jihar, Dakta labaran akan yanda ya damu da inganta harkar sayar da magunguna domin kariya ga rayuwar mutane.

Aƙarshe Shugaba Husaini ya yaba  da  goyon bayan da hukumomi irin su NAFDAC da NDLEA  da ƙungiyar PSN suke bayarwa, wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da tsarin sayar da magunguna ingantattu.

No comments