Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yi Taron Faɗakarwa Ga Malamai Da Limamai A Jihar Kaduna

Daga Imrana Abdullahi An yi kira ga ɗaukacin Malamai masu yin wa'azi da su fara da sanin manufar abin da ya sa suke yin wa'azi domin...

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga ɗaukacin Malamai masu yin wa'azi da su fara da sanin manufar abin da ya sa suke yin wa'azi domin cimma burin da ake buƙata na samun ci gaba.


Farfesa Yahaya Mijahid ne ya yi wannan kiran a wajen taron Limamai da Malamai da aka yi a ɗakin taro na Jama'atu Nasarul Islam ta ƙasa da ke Kaduna cikin makon nan. 


Farfesa Mujahid ya ci gaba da cewa, duk wanda ba shi da manufa, to haƙiƙa ba zai cimma buƙatar da ta dace a samu ba a wajen gudanar da duk wani wa'azin da ake yi.


Farfesa Mujahid ya kuma ja hankalin Malamai a lokacin wa'azi da su kauce wa tsayawa kan mayar da martani kawai a madadin yin wa'azi ga al'umma. 

Ya ƙara jaddada cewa, harkar musulunci daban da kuma wani addini can da ba na musulunci ba

Ya yi kira ga majalisar Malamai da Limamai da su fitar wa da Malamai waɗansu maudu'an da za a yi maganganu a kansu domin a samu cikakken saitin yin wa'azi.

A taron, an kuma yi kira ga majalisar Malamai da Limamai da su riƙa bibiyar irin yadda masu wa'azi ke gudanar da ayyukansu da nufin samun kyakkyawar nasarar da ake buƙata. 

A nasa jawabin, Tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna, Dokta Yusuf Arrigasiyyu, ya ce a nan da bayan Azumi za a ƙaddamar da majalisar a dukkan Ƙananan Hukumomin jihar Kaduna, da nufin samun ciyar da addinin Islama gaba ta hanyar samun haɗin kai a tsakanin al'umma. 

Dokta Arrigasiyyu ya kuma yi kira ga masu wa'azi da su mayar da hankali a kan a riƙa yin taimakekeniya a tsakanin juna, musamman a wajen ciyarwa tsakanin juna, kasancewar a halin yanzu ana cikin wani hali na maganar abinci. 

A wajen taron, an yi kira da faɗakarwa a kan irin yadda kowa ya dace ya aiwatar da wa'azi, musamman a lokacin Azumin watan Ramadana mai zuwa. An faɗakar a kan ƙa'idojin da suka dace mai yin wa'azi ya sani kafin ya zama mai hawa kan mumbarin wa'azi da nufin amfanin al'umma baki ɗaya.

 

No comments