Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sakamakon Zama Na Musamman: Shaikh Aminu Daurawa Zai Ci Gaba Da Jagorantar HISBA

Daga Musa Muhammad A halin da ake ciki dai, sakamakon wani zama na musamman da wasu Malamai suka yi da Gwamnan jijar Kano, Abba Kabir Yusuf,...

Daga Musa Muhammad

A halin da ake ciki dai, sakamakon wani zama na musamman da wasu Malamai suka yi da Gwamnan jijar Kano, Abba Kabir Yusuf, an samu sasanci, yanzu Shaikh Aminu Daurawa zai ci gaba da shugabancin Hukumar Hisba a Kano, bayan ajiye aikin da ya yi, bisa wasu kalamai da Gwamnan ya yi, waÉ—anda kuma ba su yi wa Malamin daÉ—i ba.

Bayanan da Matattarar Labarai ta tattaro, sun bayyana cewa an cimma wannan matsaya ce a wani zaman tattaunawa na musamman da wasu Malama a Æ™arÆ™ashin inuwar HaÉ—aÉ—É—iyar Ƙungiyar Malamai da Ƙungiyoyin addinin musulunci suka yi da Gwamna Abba Kabir. 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kanon, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar jiya Litini, ya bayyana cewa akwai wani zama da ya gudana tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da wata tawagar Malamai, waÉ—anda suka haÉ—a da shi kan shi Shaikh  Aminu Ibrahim Daurawa bisa jagorancin Dr. Musa Borodo da sauran Malamai irin su,  Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, Sheikh Abdulwahab Abdallah, Farfesa Salisu da sai sauransu.

A ta É“angaren gwamnati kuma, bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, akwai mataimakin sa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo; Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Alhaji Jibrin Ismail Falgore; Sakataren gwamnatin jihar, Dr Abdullahi Baffa Bichi da Shugaban Ma'aikatan gidan gwamnatin jihar,  Alhaji Shehu Wada Sagagi.

In dai ba a manta ba, a 'yan kwanakin nan ne Shugaban Hukumar ta Hisba, Shaikh Aminu Daurawa ya fito fili ya bayyana cewa a ajiye muÆ™amin nasa, wanda kuma ake jin bai rasa nasaba da wasu kalamai da Gwamnan ya yi game da yadda 'yanHusba É—in ke wuce gona da iri a gudanar ayyukan su. 

 

No comments