Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kai Hari Masallacin Juma'a a Kaduna, An Kashe Mutum Biyu

Aƙalla wasu mutane biyu ne aka kashe a lokacin sallar Juma’a a unguwar Makera da ke ƙarƙashin yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwa...



Aƙalla wasu mutane biyu ne aka kashe a lokacin sallar Juma’a a unguwar Makera da ke ƙarƙashin yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Juma’a, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Wani shugaban al’umma mai suna Hudu Kwasakwasa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ’yan bindigar sun buɗe wuta kan masu ibadar ne babu gaira, babu dalili.

“Masu ibada biyun da aka kashe na daga cikin Musulmin da aka kai wa hari a masallacin Juma’a da ke unguwar Makera a lokacin da ‘yan bindigan suka bude musu wuta tare da sace wasu a yau Juma’a. An binne waɗanda abin ya shafa a makabartar tsohon Kuyello,” inji shi.

Ya ce mutanen suna cikin raka’a na biyu na sallah a lokacin da aka kai musu hari, wanda ya tilasta wa sauran mutanen tserewa domin tsira da rayukansu.

Ya kara da cewa, a kwanakin baya, ‘yan ta'adda sun yi awon gaba da mutane kusan 9 a wata unguwa da ake kira unugwar Kanawa da ke karkashin yankin Kwasakwasa.

Ya roki agaji daga hukumomin da abin ya shafa, yana mai cewa ‘yan bindigar na kai farmaki a cikin al’umma ba tare da wata hujja ba.

Harin na baya-bayan nan kan masu ibadar ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan ‘yan bindiga sun sace ɗaliban firamare sama da 287 a ƙaramar hukumar Chikun da ke makwabtaka da jihar.

Har yanzu dai gwamnatin jihar da hukumar ‘yan sanda ba su mayar da martani kan lamarin masallacin ba, domin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ASP Mansir Hassan, an kasa samunsa a wayar tarho, kuma har yanzu bai amsa wani sako da aka aike masa na neman ƙarin haske ba.

No comments