Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ojodu LCDA Da FEBWE Sun Buƙaci A Ƙarfafa Wa Mata A Bunƙasa Kasuwanci

Daga Tanimu Muhammad, Legas Masu gudanarwa na Olusegun Odunmbaku tare da Ƙungiyar Mata ’Yan Kasuwa, FEBWE, sun gudanar da wani taron ƙara wa...


Daga Tanimu Muhammad, Legas

Masu gudanarwa na Olusegun Odunmbaku tare da Ƙungiyar Mata ’Yan Kasuwa, FEBWE, sun gudanar da wani taron ƙara wa juna sani kan sha’anin bunƙasa kasuwanci mata a wani ɓangare na bikin ranar mata ta duniya a Ojodu LCDA, inda suka nemi da a tallafa wa mata wajen bunƙasa harkar kasuwancin su. 

An gudanar da taron ne da niyyar ƙarfafa mata a Ojodu LCDA da kuma ƙarfafa su shiga cikin kasuwanci da ci gaban zamantakewa, wanda ya gudana a garin Legas cikin makon nan.

Taron ya samu halartar manyan daban-daban daga Febwe da masu fafutuka kamar jakadaniyar Ghana waɗanda suka ba da labarin abubuwan da suka fuskanta da gogewarsu kan ƙarfafa mata da kasuwancin su. Sun tattauna irin ƙalubalen da mata ke fuskanta wajen fara sana’a da gudanar da sana’o’i tare da bayar da bayanai masu ma’ana kan yadda za a shawo kan waɗannan ƙalubale.

Shugabar FEBWE ta ƙasa, Omotola Omole da ƙaramar jakadiyar Ghana, Misis Samantha Gift Bukhari sun kuma bayyana muhimmancin shigar da mata dukkan al’amura, tun daga ilimi zuwa aikin yi da jagoranci, sun kuma jaddada buƙatar samar da damadmaki ga mata da kuma sanin irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma.


Shugabar ƙungiyar Ojodu LCDA, Misis Abimbola Odunmbaku wadda ita ma ta samu ƙaddamar da ƙungiyar ta FEBWE ta ce ƙarfafa wa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci, da kuma neman daidaiton jinsi yana wargaza shingen da ke kawo cikas ga ci gaban mata a harkokin kasuwanci.

No comments