Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiya ne sun kai hari ƙauyen Gidan Bakuso da ke yankin Ƙaramar Jukumar Gada a Jihar S...
Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiya ne sun kai hari ƙauyen Gidan Bakuso da ke yankin Ƙaramar Jukumar Gada a Jihar Sakkwato tare da sace ɗaliban wata tsangaya.
Rahotonni na cewa maharan sun far wa garin ne da tsakar daren ranar Juma'a lokacin da ɗaliban ke barci.
To amma kakakin rundanar 'yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce rundunar ba ta da labarin harin, amma tuni ta tura jami'anta zuwa yankin don tabbatar da ainihin abin da ya faru.
No comments