Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Kawo Ƙarshen Yanayin Da Al'umma Ke Ciki - Majalisar Wakilai

   Daga Imrana Abdullahi Shugaban Majalisar wakilai ta tarayya, Dokta Abbas Tajuddeen ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa sun je majalisar...

 

 Daga Imrana Abdullahi

Shugaban Majalisar wakilai ta tarayya, Dokta Abbas Tajuddeen ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa sun je majalisar ne a matsayin wakilan jama'ar da suka zaɓo su, ba wai suna wakiltar kawunansu ba ne ko sun je majalisar domin biyan buƙatun kans u kawai.

Dokta Abbas Tajuddeen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen wani taron manema labarai na duniya da majalisar ta yi a Abuja.

"Muna sane da irin halin rayuwar da jama'a ke ciki, kuma mu ma muna jin irin yanayin da kowa ke ciki, don haka muna ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar da ikon Allah".

Akwai wani babban taron da za mu kira domin a tattauna hanyoyin ƙara inganta al'amuran ƙasa, kuma za a yi wannan taron tattaunawa ne domin lalubo hanyoyin samar da ci gaban pasa tare da al'umma baki ɗaya.

Rashin yi wa jama'a bayani ke haifar da matsalar jita-jita a duk abin da Gwannati ke ƙoparin yi, musamman a game da batun ɗaukar waɗansu ɓangarorin babban Bankin ƙasa na CBN zuwa Legas, rashin yin bayanin dalilin hakan ne ya haifar da samun jita-jita.

"Don haka ne nake yin kira ga dukkan ɓangarorin Gwamnatin oasa da su riƙa yi wa jama'a bayanin duk abin da za a yi ta yadda za a magance matsalar yan haifar da jita - jita".

Abbas ya ci gaba da cewa wannan babban taron manema labarai na pasa shi ne na farko kuma hakan shi ne wani ɓangare na samar da canjin da ake buƙata, ba tare da jin komai ba muna tabbatarwa da jama'ar ƙasa cewa babu wata tantama za a samu dukkan ci gaban ƙasa da kowa ke buƙata.

"Muna yi wa 'yan Nijeriya albishirin cewa majalisa  ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da ci gaban da ake buƙatar samu a Nijeriya. 

Shugaban majalisar ya dai amsa dukkan tambayoyin manema labarai da suka yi masa a wajen wannan babban taron manema labarai na duniya da majalisar wakilan ta yi.

No comments