Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Sanda Sun Ja Kunnen Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

  Daga Musa Muhammad Rundunar 'yan sanda a jihar Oyo sun ja kunnen masu shirya zanga-zana game da halin tsadar rayuwar da ake ciki da su...

 

Daga Musa Muhammad

Rundunar 'yan sanda a jihar Oyo sun ja kunnen masu shirya zanga-zana game da halin tsadar rayuwar da ake ciki da su yi taka-tsantsan game da masu neman juya abin ya zama wani abu, wanda ta ce ba za ta lamunta ba. 

Don gudun haka, sai rundunar 'yan sandan ta shawarci ɗaiɗaikun jama'a ko ƙungiyoyin da ke son shirya Zanga-Zangar, su sanar da rundunar a rubuce don ta samar da tsaro, kada ɓata gari ƙwace abin. 

Cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar, Yemisi Opalola ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, “Bayanin sirri ya iske mu cewa wasu na neman fakewa da tsadar rayuwa, suna son fitowa Zanga-Zanga a jihar nan. 

“A saboda haka ne rundunar nan ke amfanin da wannan dama wajen jawo hankalin waɗannan mutane su janye wannan shiri nasu da ka iya kawo ɓarkewar rikici a jihar. 

“Yana da muhimmanci a sani cewa akwai wasu ɓata gari da ke shirin  shiga wannan Zanga-Zanga don kawo yamusti a jihar nan."

Daga nan sanarwar ta jawo hankalin jama'ar jihar, kan cewa kowa ya ci gaba da harkokin sa na yau da kullum, domin rundunar ta ɗauki duk matakan da suka wajaba don daƙile duk wata barazana. 

No comments